Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sashen Ilimin Manyan Makarantu


Gabatarwa

Sashen Ilimin Manyan Makarantu (Department of Tertiary Education), sashe ne a Hukumar Ilimin Tarayyar Najeriya (Federal Ministry of Education), wanda aka ƙirƙire shi a shekarar 2000. Tsohon sashen Ilimin Zamani (Department of Formal Education) aka rikiɗar zuwa wannan sashe; wato kamar canjin suna aka yi tare kuma da ƙarin ayyuka daga na biyu zuwa na farko.

Asalin nauyin da aka ɗora wa wannan sashe shi ne kula da harkokin ilimin jami’o’i. Sai kuma a watan Mayu na 2003, da aka sake ƙara masa ɗawainiyoyin da suka shafi harkokin ilimin sauran manyan makarantu waɗanda ba jami’o’i ba ƙari a kan aikinsa na farko.  Saboda haka sai aka canja sunan ya koma kamar yadda yake a yanzu; Sashen Ilimin Manyan Makarantu (Department of Tertiary Education) sakamakon sake sabunta shi da aka yi kamar yadda muka naƙalto daga shafin Hukumar Ilimi ta Tarayyar Najeriya wanda aka wallafa a shekarar 2017.

Ayyuka

Ayyukan wannan sashe sun haɗa da:

  1. Tsara ƙa’idodi, sada-tsakani (Coordinating), aiwatar da su da kuma kula da su.
  2. Samar da sababbin manyan makarantun ilimi da kuma karɓe ragamar ci gaba da kula da waɗanda ake da su ta hanyar haɗin guiwa da hukumomin da suke da alaƙa.
  3. Kula ko saka ido a kan rassan da suke sashen manyan makarantu.
  4. Sada-tsakani a fannin rawar da duba-gari (Visitors’) za su taka a Manyan Makarantun Gwamnatin Tarayya.
  5. Shiryawa (Organizing) da kuma sada-tsakanin Tawagar Duba-Gari (Visitation Panels) zuwa ga Manyan Makarantun Ilimi na Gwamnatin Tarayya bayan dukkan shekaru huɗu-huɗu bisa dacewa da tsarin doka.
  6. Shirya shiftar (Drafting) takardun rahoto daga jawaban (Recommendations) da aka rairayo daga rahotannin Tawagar Duba-Gari.
  7. Rarrabawa da kuma saka-ido a kan wakilan hukuma a Majalisun Gudanarwa (Governing Councils) na Manyan Makarantun Tarayya da kuma hukumar (Board) rassan (Parastatals) Humukar Ilimi ta Tarayya.
  8. Sada-tsakani a cikin al’amuran Ƙungiyoyin Ma’aikata (Staff) da na Ɗalibai.
  9. Bayar da lasisin gudanar da manyan makarantu masu zaman kansu da suka haɗa da Makarantun Ƙirƙirar Sana’o’i (Innovation Enterprise Institutions) tare da haɗin guiwar Hukumomin da suke kula da harkar.
  10. Samar da gurbin bayar da shawara da kuma waiwaitar ayyukan manyan makarantun jahohi da kuma masu zaman kansu.
  11. Sada-tsakani a harkokin da suka shafi dangantaka da ƙasashen waje a sashen Ilimin Manyan Makarantu.
  12. Ɗaukaka kukkutsawa da kuma amfani da Fasahar Sadarwa da Bayanai (ICTs) a Manyan Makarantun Ilimi kamar abin da ya shafi tattara bayanai (Data Collection) da sauransu.

Rassa

Wannan sashe yana da rassan da suke ƙarashin kulawarsa da suka haɗa da:

  1. Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (National Universities Commission (NUC)).
  2. Hukumar Ilimin Fasaha ta Ƙasa (National Board for Technical Education (NBTE)).
  3. Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa (National Commission for Colleges of Education (NCCE)).
  4. Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a da Manyanyan Makarantu (Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB)).
  5. Hukumar Yi Wa Malamai Rijista ta Nijeriya (Teachers’ Registration Commission of Nigeria (TRCN)).
  6. Amintacciyar Hukumar Ɗaukar Ɗawainiyar Ilimin Manyan Makarantu. (Tertiary Education Trust Fund (TETFUND)).
  7. Babbar Makarantar Horas da Malaman Makaranta ta Ƙasa (National Teachers’ Institute (NTI)).
  8. Ƙauyen Harshen Faransaci na Nijeriya (Nigerian French Language Village (NFLV)).
  9. Ƙauyen Harshen Larabci na Nijeriya (Nigerian Arabic Language Village (NALV)).
  10. Cibiyar Lissafi ta Ƙasa (National Mathematical Centre (NMC)).
  11. Makarantar Harsunan Nijeriya ta Ƙasa (National Institute of Nigerian Languages (NINLAN))

Ƙungiyoyin Malamai da na Ma’aikatan Manyan Makarantun Nijeriya

  1. Kwamatin Shugabannin Jami’o’i (Committee of Pro-Chancellors (CPC)).
  2. Kwamatin Mataimakan Shugabanin Jami’o’i (Committee of Vice-Chancellor (CVC)).
  3. Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (Academic Staff Union of Universities (ASUU)).
  4. Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya (Senior Staff Association of Nigerian Uniɓersities (SSANU)).
  5. Ƙungiyar Ma’aikatan da Ba Malamai ba ta Jami’o’i (Non-Academic Staff Union of Uniɓersities (NASU)).
  6. Ƙungiyar Malaman Fasaha ta Ƙasa (National Association of Academic Technologists (NAAT)).
  7. Kamfanin Sarraffa Fanshon Jami’o’i na Najeriya (Nigerian University Pension Management Company (NUPEMCO)).
  8. Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Fasaha (Academic Staff Union of Polytechnics (ASUP)).
  9. Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Makarantun Fasaha (Senior Staff Association in Nigerian Polytechnics (SSANIP)).
  10. Ƙungiyar Ma’aikatan da Ba Malamai ba ta Makarantun Ilimi da Dangoginsu (Non- Academic Staff Union of Educational & Associated Institutions (NASU)).
  11. Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi (Colleges of Education Academic Staff Union (COEASU)).
  12. Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Kwalejojin Ilimi ta Najeriya (Senior Staff Union Colleges of Education, Nigeria (SSUCOEN)).
  13. Ƙungiyar Ma’aikatan da Ba Malamai ba ta Makarantun Ilimi da Dangoginsu (Non-Academic Staff Union of Educational & Associated Institutions (NASU)).

Manazarta


Federal Ministry of Education (2017). Federal Ministry of Education–Department of Tertiary Ecation. AN ciro daga shafin: http://www.education.goɓ.ng a shekarar 2018.

Servicom (2017). Federal-Ministry-of-Education. An ciro daga shafin: http://servicom.gov.ng/wp-content/uploads/2017/09/Federal-Ministry-of-Education.pdf a shekarar 2018.


Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Alamomi da Tambari

Hukumomi da Rasssan Gwamnati


Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub